fbpx
Monday, August 8
Shadow

Abuja da wasu Jihohi 20 na iya fuskantar matsalar karancin abinci – Rahoton

Rahoton ya kuma bayyana cewa kimanin mutane miliyan 14.4 da suka hada da ‘yan gudun hijira 385,000 a jihohi 20 da kuma babban birnin tarayya Abuja sun riga sun shiga cikin mawuyacin hali na karancin abinci, wanda zai iya kai har watan Mayun 2022.

Binciken Cadre Harmonisé (CH) wani kayan aiki ne na haɗe-haɗe don nazarin matsanancin rashin abinci da abinci mai gina jiki, a cikin jahohin Sahel 17 da Yammacin Afirka ciki har da Najeriya.

A Najeriya, ma’aikatar noma da raya karkara ta tarayya, hukumar abinci da noma ta Majalisar Dinkin Duniya FAO, da hukumar samar da abinci ta duniya WFP, da sauran masu ruwa da tsaki ne suka hada shi tare.

Karanta wannan  Rundunar sojoji hadin kai sun hallaka 'yan bindiga takwas a jihar Filato

Rahoton ya kunshi jihohi 21: Abia, Adamawa, Bauchi, Benue, Borno, Cross-River, Edo, Enugu, Gombe, Jigawa, Kaduna, Kano, Katsina, Kebbi, Lagos, Niger, Plateau, Sokoto, Taraba, Yobe, Zamfara da kuma babban birnin tarayya Abuja.

Rahoton ya yi nuni da rashin tsaro, musamman a Arewa maso Gabas, hauhawar farashin kayayyaki, hauhawar farashin kayan masarufi da kuma raguwar kudaden shiga na gida sakamakon dadewar da annobar COVID-19 ta haifar a matsayin jiga-jigan matsalar karancin abinci.

Dan sauke manhajar hutudole a wayoyin ku. Sai a bi wannan link din na kasa:

Leave a Reply

Your email address will not be published.