fbpx
Tuesday, July 5
Shadow

Abuja: Mazauna Gwagwalada sunyi kira da gwamnati data rushe gidajan dake kan magudanan ruwa

Wasu mazauna karamar Hukumar Gwagwalada, Babban Birnin Tarayya (FCT) a ranar Alhamis sun yi kira ga gwamnati da ta rushe gidaje da aka gina a kan hanyoyin ruwa don kauce wa ambaliyar ruwa na shekara-shekara nan.

Mazauna garin da abin ya shafa sun yi wannan kiran ne sakamakon ruwan sama da aka yi ranar Juma’ar da ta gabata wanda ya haifar da ambaliyar ruwan da ke haifar da asarar dukiya da asarar rayuka.

Mista Kolade Akinsoju, mazaunin Gwagwalada ya fada wa Kamfanin Dillancin Labarai na NAN a Abuja cewa suna tuna yadda ruwan sama ya haifar da asarar rayuka da dukiyoyi.

Akinsoju ya ce dalilin ambaliyar ya kasance sakamakon gidajen da aka gina akan hanyoyin ruwa ba tare da sanya tsarin magudanan ruwa ba.

Dan sauke manhajar hutudole a wayoyin ku. Sai a bi wannan link din na kasa:

Leave a Reply

Your email address will not be published.