Wani daya daga cikin alhazan Najeriya ya mayarwa hukumar alhazai ta kasa NAHCON da ke Madinah ta kasar Saudiyya jakar kudin da ya bata dauke da dalar Amurka 700, N70,000 da kuma Riyal 4 na kasar Saudiyya kimanin N360,000.
Rahotanni sun bayyana cewa, Mutumen ya fito ne daga karamar hukumar Tambuwal a jihar Sokoto.
Ya ce ya tsinci jakar ne a matakalar masaukin su a otal inda alhazan jihohin biyu ke kwana.
An ce mai jakar da ya bata, alhajin jihar Kaduna ne a Madina.
A nasa jawabin, Bakaya ya bayyana cewa bai yi nadamar mayar da kudin ga mai shi ba domin ba hakkinsa ba ne.