Wednesday, June 3
Shadow

Abun mamaki: Messi ya bayyana a karo na farko cewa ya so barin Barcelona

Lionel Messi ya kasance a Barcelona na tsawon shekaru 18 kuma yayi nasarar samun dukkan wani abu da dan wasa yake kwadayi a duniyar wasan kwallon kafa.

An yankewa Messi hukuncin watanni 21 a gidan yari bayan an kama shi tare da mahaifin shi Jeorge da laifin yiwa kasar Spain zamba cikin amince wurin biyan kudin haraji na kusan euros miliyan 4.1 tsakanin shekara ta 2007-2009. An sassautawa Messi hukuncin yayin da aka bukaci ya biya euros 252,000.
A wata ganawa da Messi yayi da RAC1, ya bayyana masu cewa zai bar kungiyar Barcelona saboda cin fuskar da gwamnatin Spain suka yi mai. Sai dai Messi yace zai tafi amma ba saboda yana so ya bar Barcelona ba saboda kasar Spain zai tafi.
Messi yace an ci mai fuska saboda haka ba zai cigaba da zama a kasar ba, kuma bai taba samun wata kwantiraki mai tsoka ba saboda kowa ya san bai da ra’ayin barin kungiyar Barcelona.
Yanzu kuma Messi ya tabbatarwa da RAC1 cewa zai cigaba da wasa a Barcelona har sai yayi ritaya.

Dan sauke manhajar hutudole a wayoyin ku. Sai a bi wannan link din na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=hdlabarai.aplibwxLeave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *