Daga Babangida Ibrahim
A lokacin mulkin Olusegun Obasanjo musamman a shekaru huɗun farko, Atiku ya kasance shi ke juya akalar gwamnatin Obasanjo, domin kusan dukkanin gwamnoni da Ministoti nashi ne, a fagen siyasa ma anfi jin muryar sa fiye da ta shugaba Obasanjo.
A takaice dai a tarihin Najeriya Atiku shine mataimakin shugaban ƙasa da ya samu damar da babu wani mataimakin shugaban ƙasar da ya taɓa samun kwatankwacin ta.
Duk da kasancewar Atiku ɗan yankin Arewa maso gabashin Najeriya, hakan bai sanya shi yiwa yankin abun gani da faɗa ba a lokacin da yayi kane-kane a madafun iko.
A wancan lokaci Atiku yana da damar gina Arewacin Najeriya ba iyaka yankin Arewa maso gabas ba, amma sai dai babu abunda ya gina a yankin Arewa maso gabas ballantana Arewa baki ɗaya.
Ko a jihar Adamawa babu kwakkwaran aiki da Atiku ya yiwa jihar wanda zasu bugi kirji suce ɗansu ya yi wannan aiki sakamakon matsayin da ya samu na mataimakin shugaban ƙasa.
A takaice dai hanyar shiga ƙaramar hukumar da aka haife shi, shugaban kasa Buhari ne yayi ta, hanyar zuwa jihar sa Adamawa ma shugaba Buhari ne ya sabunta ta bayan taci rayukan dubban jama’a.
Waɗannan dalilai na rashin yiwa yankin sa Rana, kan iya zama silar faɗuwa zaɓensa a yankin.