Mun samu ƙarin bayani game da adadin alhazan Najeriya da suka isa Saudiyya don gudanar da aikin Hajji na shekarar Hijira 1443 – 2022.
Jumillar adadin waɗanda suka sauka a Madina sun kai 1,354, kamar yadda Hukumar Aikin Hajji ta Ƙasa ta bayyana.
Daga cikin adadin, 171 maza ne, sai kuma mata 176.
An samu ƙarin adadin ne bayan jirgin FLYNAS XY5002 ya tashi da alhazai 347 da jami’ai 23 daga filin jirgin sama na Abuja a yau Asabar.