Saturday, July 13
Shadow

Addu’a ga masoyiyata

Ina fatan Allah ya haskaka rayuwarki.

Fatana shine ki fi kowa a tsakanin sa’anninki.

Allah yasa mu zama mata da miji.

Allah yawa soyayyarmu Albarka ta yanda zamu yi aure mu haifi ‘ya’ya masu Albarka.

Ina fatan Allah ya kareki daga sharrin makiya, Mahassada da kambun baka, masoyiyata kada ki manta da karanta falaki da Nasi safe da yamma.

Kina da kyau, dan haka nasan akwai mahassada da masu mugun baki, fatana shine Allah ya kareki daga dukkan sharrinsu.

Kina da Basira, Fatana shine Allah ya kareki daga sharrin mahassada.

Babyna ki kasance kullun cikin zikiri, zaki rabauta daga sharrin shedan la’ananne.

Karanta Wannan  Yadda ake ma saurayi shagwaba

Insha Allahu duk inda zaki shiga sai Allah ya hadaki da masoya na gaskiya.

Babban burina shine inga Allah ya daukakaki a tsakanin sa’anninki.

Masoyiyata Ki rike salati dan samun ceton ma’aiki ranar gobe kiyama.

Kin matukar birgeni inda nakira waya baki dauka ba kikace min sallah kike, ko kuma idan muna waya kika tunatar dani cewa lokacin sallah yayi, ina fatan Allah ya karba mana ibadunmu.

Ina matukar Alfahari dake idan muna waya kika yanke kika ce mama na kiranki, ko kina dauka kikace min kina aikine, zamu yi waya anjima, ko baki dauka ba amma kika bani uzurin cewa, kinawa mama aiki ne, wannan alamace ta kin samu tarbiyya me kyau da sanin darajar iyaye da ta sauran mutane, ina fatan Allah ya karba miki.

Karanta Wannan  Addu ar maganin mantuwa

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *