Friday, July 12
Shadow

Addu’ar samun mijin aure da gaggawa

Ga me neman matar aure ko mijin aure, akwai addu’o’i da malamai na sunnah suka kawo wanda ke taimakawa wajan kawo nesa kusa.

Addu’a ta farko itace Rabbana Atina Fidduniya hassana wafil Akirati Hassana, wakinna Azabannar.

Wannan addu’a ta game kowace irin bukata mutum ke nema a Duniya da Lahira, kuma kusan duk musulmi ya santa amma wani yana ganin kamar ta yi kadan.

Malaman Sunnah sun tabbatar da naci da yakini da sakankancewa ana wannan addu’a na kawo biyan bukata.

Sai kuma Addu’a ta biyu.

Itace “La’ilaha illallahul Azimul halim, La’ilaha illallahul hakimul Karim, La’ilahaillalah, Subhanallah, Rabbissamawatissaba’i wa rabbularshilazim, Alhamdulillahi rabbil alamin”

Karanta Wannan  Addu'a ga masoyiyata

Itama wannan addu’a idan aka haddace ta ana yinta akai-akai tana kawo nesa kusa.

Akwai kuma addu’ar la’ilahailla Antassubhanaka inni kuntu minazzalimina.

Itama addu’ace wadda idan mutum na cikin kunci ko tsananin bukata, idan yagi ta zai samu mafita insha Allah.

Allah yasa mu dace.Ku biyomu a shafukanmu na sada zumunta dan samun labarai masu kayatarwa:

A shafin twitter zaku same mu a @hutudole

A shafin Facebook zaku samemu a @hutudolehausa

Danna nan dan sanin yanda zaku tallata hajarku a shafin hutudole

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *