Haramtacciyar kungiyar IPOB ta gargadai dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar NNPP, Sanata Rabi’u Musa Kwankwaso cewa ya daina danganta su da Peter Obi.
Mai magana da yawun kungiyar, emma Powerful ne ya bayyana hakan inda yace su ba ruwansu da dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar Labour Party, wato Peter Obi,
Domin bai taba taimaka masu ba a fafutukar da suke yi ta neman ‘yanci ba saboda haka ahir din Kwankwaso ya daina dangantasu da Obi.
A karshe Emma yace su ba ruwansu da irin siyasar da kasa Najeriya keyi a yanzu.