fbpx
Wednesday, May 25
Shadow

Ahmad Indimi, Mijin Zahara Buhari yayi murnar cikarsu shekara daya da yin aure:” Nayi sa’ar mata: Ina alfahari da kasancewa mijinki”>>injishi

Ahmad Indimi, mijin diyar shugaban kasa, Zahara Buhari, ya bayyana jin dadinshi da murna bisa cikarsu shekara daya da yin aure, Ahmad ya bayyana cewa a gaskiya yayi sa’ar mata, kuma yana alfahari da kasancewa mijin Zahara.


(adsbygoogle = window.adsbygoogle || []).push({});

A wani sako daya fitar ta dandalinshi na sada zumunta da muhawa, Ahmad yayi bayani kamar haka:

“wow, kai har anyi shekara guda(da yin bikinmu). Shekara daya da nayi tare da ke(Zahara Buhari) itace shekara mafi kyau a shekarun rayuwata. Masu iya magana na cewa, idan bakayi sa’ar mace ba to ka kade/kashinka ya bushe. Amma idan kayi sa’ar mace, to ka zama cikakken mutum(me nutsuwa). Zan biki kirji in fadi cewa samuwarki a cikin rayuwata tasa na zama cikakken mutum. Abin jin dadi da alfaharine kasancewata mijinki. Ina sonki, Zahara Buhari”.

Muna tayasu murna da fatan Allah ya albarkaci wannan aure nasu ya kuma kara dankon soyayya.


(adsbygoogle = window.adsbygoogle || []).push({});

Karanta wannan  'Wasu 'Yan Nijeriya Sun Kama Kifi Mafi Sauri A Duniya Wanda Kudinsa Ya Haura Naira Dubu 600 Amma Sun Dafe Shi Sun Cinye

Dan sauke manhajar hutudole a wayoyin ku. Sai a bi wannan link din na kasa:

Leave a Reply

Your email address will not be published.