Dan wasan gaba na kungiyar Al Nassr ya zamo dan wasan Najeriya na farko daya fara cin kwallaye guda biyu a cikin wasa daya na gasar kofin duniya ta FIFA, yayin da yayi nasarar jefa kwallaye guda biyu a wasan da Najeriya ta buga tsakanin su da Argentina a kasar Brazil shekara ta 2014.
Kuma yaci kwallaye biyu a wasan da suka buga da Iceland a kasar Russia shekara ta 2018. Ya kasance daya daga cikin yan wasan Najeriya masu arziki kuma yana daukar albashin Naira biliyan 1.2 a kowace shekara.
https://www.instagram.com/p/B_z7SpIjoya/?igshid=1q86dg84xr24s
Dan wasan mai shekaru 27 ya saka hoton wata hamshakiyar mota daya siya mai suna G Wagon Benz a shafin shi na twitter. kungiyar Al Nassr sun siya Ahmad Musa daga kungiyar Leicester City a shekara ta 2018 kuma dan wasan yayi nasarar jefa kwallaye har guda tara a wasanni guda 48 daya buga. Kuma ya taimakawa gasar Saudi premier lig da Saudi super cup a shekara ta 2019.