Tauraron dan kwallon Najeriya, Ahmed Musa na shirin barin kungiyar Kano Pillars bayan samun kungiyar kasar Turkiyya da zata daukeshi.
Ahmed Musa zai shiga yarjejeniyar €2.2m, Kwatankwacin Naira Biliyan 1.05 tsawon shekara 1 da kungiyar.
Wakilin Musa ya bayyana cewa kungiyar da farko ta baiwa Musa Kwantirakin €2m amma yaki amincewa, daga baya ta kara masa €2.2, tace saboda matsin tattalin arzikin da coronavirus ta kawo ne ya jawo haka, kamar yanda Leadership ta ruwaito.