fbpx
Friday, February 26
Shadow

Aika-aika ne tsantsa yunkurin Gwamnatin Kano na rushe gadar kofar Nasarawa>>ja’afar Sani Bello

Ɗan siyasar nan da ya nemi jam’iyyar PDP ta tsayar da shi takarar gwamnan jihar Kano a zaɓen shekara 2015 Jafar Sani Bello ya bayyana ƙudurin gwamnatin jihar Kano na rushe gadar sama ta ƙofar Nasarawa a matsayin aika – aika kuma awon igiya.

 

Jafar Sani Bello wanda ya yi shuhura wajen bayyana raayinsa a fili ba tare da tsoro ba, musamman a gwamnatin Muhammad Buhari,

 

Ja’afar ya bayyana hakan ne a shafinsa na facebook a matsayin martani ga shirin gwamnatin jihar Kano na rushe gadar saman.

 

Ya kara da cewa “Rushe gadar Kofar Nassarawa Yanzu aika-aika ne, awon Igiya” In ji Jafar Sani Bello.

 

Wannan dai yana zuwa ne a dai-dai lokacin da al’ummar jihar Kano ke bayyana ra’ayoyinsu akan gadar.

Dan sauke manhajar hutudole a wayoyin ku. Sai a bi wannan link din na kasa:


×
Kano

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *