fbpx
Wednesday, May 25
Shadow

Aikin hajjin bana na 2022 zai yi tsada sosai, kuma duk wanda ya wuce shekaru 65 ba zai je ba>>NAHCON

Hukumar kula da aikin Hajji ta Najeriya, NAHCON ta bayyana cewa, kudin aikin hajjin bana zai yi tsada sosai.

 

Shugaban hukumar, Alhaji Zikrullah Hassan ne ya bayyana haka a Babban birnin tarayya, Abuja ranar Alhamis inda yace dalilan hakan a bayyane suke.

 

Hakanan ya kuma bayyana cewa, duk wanda ya haura shekaru 65 ba zai halar aikin hajjin banan ba.

 

Yace da farko za’a biya kudin aikin hajjin akan farashin dala $410 maimakon dala $360 da aka biya a shekarar 2019.

 

Yace farashin aikin hajji ya dogara ne ga farashin canjin kudi.

 

Yace hakanan kasar Saudiyya ta kara kudin harajin VAT wanda yace shima zai sa kudin aikin hajjin ya karu.

 

Yace kuma a ganawarsu da wakilan kasar Saudiyya, sun gaya musu cewa, farashin kudin aikin hajji zai karu sosai saboda sun kashe kudi sun yi kyare-kyare a guraren Ibada.

Dan sauke manhajar hutudole a wayoyin ku. Sai a bi wannan link din na kasa:

Leave a Reply

Your email address will not be published.