Tauraruwar fina-finan, Saratu Gidado wadda aka fi sani da Daso data shahara wajan fitowa a matsayin uwa ta yabawa shugaban kasa,Muhammadu Buhari kan aikin da yake.
A cikin wani sako da Daso ta saki ta shafinta na sada zumunta ta bayyana cewa”Shugaban kasar Najeriya kenan, Muhammadu Buhari. Allah ya dada Kareka a duk inda kake.”
“Aikinka na yin kyau na bada tallafi ga ‘yan kasa, da bankado masu laifuka, da hukunta masu wadaka da kudaden Talakawa”
Daso dai na daya cikin masoya shugaban kasa, Muhammadu Buhari na Masana’antar Kannywood.