fbpx
Thursday, July 7
Shadow

Aikin shedancine kisan da aka yi a jihar Filato>>Shugaba Buhari

Shugaban kasa, Muhammadu Buhari ya bayyana cewa, kisan da aka yi a Kanam dake jihar Filato aikin shedancine.

 

Shugaban ya bayyana hakane a sanarwar da ya fitar ta hannun kakakinsa, Malam Garba Shehu, ya kuma mika sakon ta’aziyya ga iyalan mamatan.

 

Shugaban kasa, Muhammadu Buhari yace, sojoji kada su yafewa ko kuma su kyale Wanda suka yi wannan aika-aika.

 

Shugaban ya kuma kara da cewa, yana kira ga mutanen garin da su bayyana wadanda suka yi wannan aikin shedanci.

Leave a Reply

Your email address will not be published.