fbpx
Thursday, February 9
Shadow

AISHA BUHARI: Ni Ma Ba Zan Iya Daukar Wulaƙancin Yaran Soshiyal Midiya Marasa Tarbiyya Ba, Cewar Mansurah Isah

AISHA BUHARI: Ni Ma Ba Zan Iya Daukar Wulaƙancin Yaran Soshiyal Midiya Marasa Tarbiyya Ba, Cewar Mansurah Isah

DAGA ABBA MUHAMMAD

Tsohuwar jaruma a Kannywood kuma furodusa, Mansurah Isah, ta ja kunnen mutane da kada wanda ya ce ta yi magana a kan matar shugaban ƙasa, A’isha Buhari.

A wannan makon dai muhawara ta ɓarke kan shari’ar da ake yi tsakanin matar shugaban ƙasar da wani ɗalibin jami’a da ya faɗi baƙar magana a kan ta a Twitter.

Aisha Buhari ta maka shi a kotu bayan jami’an tsaro sun kamo shi sun kawo shi Abuja.

Mansurah ta yi maganar ne a Instagram, inda ta ɗora hoton rubutun da ta yi da Turanci. Mujallar Fim ta fassara rubutun kamar haka: “Kada wanda ya tambaye ni in ce wani abu a kan A’isha Buhari. Ni ma na taɓa shiga wannan halin. Haka ‘ya ta ma ta taɓa shiga irin wannan halin. Na ce a’a da cin mutuncin soshiyal midiya da kalaman ƙiyayya.

“Ni ba matar shugaban ƙasa ba ce ko iyalin sa. A matsayi na na ‘yar wasa, na san yadda mu ke ji, inda wasu wawaye, marasa kunya, mahaukatan mutane, su kan zo soshiyal midiya, su na faɗin abubuwa a kan mu, su zage mu, su kira mu da sunaye kala-kala.

“Wasu lokuta mu yi kuka a ɓoye. Manyan jaruman duniya da ba za su iya ɗauka ba, kan kashe kan su.

“Ba zan kashe kai na ba, amma ba zan taɓa barin wanda ba shi da tarbiyyar gida ya yi wasa da rayuwa ta ko lafiya ta ba. Za su yi basaja da sunan ka, su ɗora bidiyon marasa lafiya a matsayin kai ne.

“Wallahi, wallahi, abin da ciwo, har ta kai ƙarshe, na kai wasu marasa kunya gidan yari. Ba zan ɗaukar wa kai na ko iyali na ba. Kada ku taɓa ni, shi kenan.”

A ƙasan hoton da ta ɗora ɗin kuma, sai ta rubuta cewa, “Ƙananan yara za su zo soshiyal midiya su zage ka, su ci mutuncin ka, su ci zarafin ka da sauran su.

“Haka kawai, ba abin da ka yi musu don su na ganin sun isa, ba a isa a yi musu komai ba.

“Za su buɗe yanar gizo da sunan ka, su rinƙa ‘posting’ ɗin batsa, satar kuɗin mutane da ɓatanci da sunan ka. Sannan a ce kar ka ɗauki mataki, haba jama’a, mu rinƙa yi wa junan mu adalci!”

“Ɓatanci a ‘social media’ addini ne?

“Munafukin mutum ɗan ‘social media’ (like influencer na social media) shi ne zai ce ba a yi daidai ba.”

“Akwai wata kwanaki da su ka biyo ta har cikin ‘dm’ (diract message) ɗin ta su na cin zarafin ta, wallahi sai da ta kwanta a asibiti.

“Ni ce nan na yi mata wa’azi cewa sai haƙuri kawai da yi musu Allah ya isa.”

Dan sauke manhajar hutudole a wayoyin ku. Sai a bi wannan link din na kasa:

Talla: Danna nan dan samun gagarumar kyauta

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *