fbpx
Thursday, February 9
Shadow

Aisha Buhari ta janye kararda ta kai Aminu Muhammad

Aisha Buhari ta janye kararda ta kai Aminu Muhammad, lawyansa C.K. Agu ya shaida wa BBC.

Matar Shugaban Najeriya Aisha Buhari ta janye ƙara da kuma tuhumar da take yi wa ɗalibin nan Aminu Muhammad, kamar yadda lauyansa ya shaida wa BBC Hausa.

Cikin wani saƙon tes, Barista C.K. Agu bai yi ƙarin bayani ba game da dalilin da ya sa Aisha ta janye ƙarar.

Matakin na zuwa ne bayan ɗalibin ya shafe kwana uku a gidan yari da ke Suleja bisa umarnin kotun.

Karanta wannan  Hotuna da Bidiyo Da Duminsa: Zanga-zangar rashin man fetur da Kudi ta barke a Abeokuta

A ranar Litinin ake sa ran ci gaba da zaman kotun don sauraron neman beli da lauyan Aminu ya yi a zaman ranar Talata da aka yi, wanda bai yi nasara ba..

Matar shugaban na zargin Aminu da ɓata mata suna saboda saƙon da ya wallafa a shafinsa na Twitter maƙale da hotonta tare da cewa “ta ci kuɗin talakawa”.

Dan sauke manhajar hutudole a wayoyin ku. Sai a bi wannan link din na kasa:

Talla: Danna nan dan samun gagarumar kyauta

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *