fbpx
Saturday, May 21
Shadow

Aisha Buhari ta yi wa ‘yan Zamfara addu’a

Uwargidan shugaban Najeriya Aisha Muhammadu Buhari ta wallafa wani sako a shafinta na Facebook inda a ciki ta yi wa al’ummar jihar Zamfara ta arewa maso yammacin kasar addu’ar zaman lafiya.

Aisha Buhari ta wallafa sakon ne da misalin karfe 12:09 na daren Laraba, inda ta roki Allah ya samar wa mutanen jihar – har da sauran ‘yan kasar – mafita daga matsalar tsaron da ta addabe ta, musamman a lokacin da Musulmi ke raya dare domin neman falalar Lailatul Kadri:

“Allah ya fitar da mu da mutanen jihar Zamfara daga chikin wannan hali, albarkacin daren Lailatul Kadri, Ameen!”

Baya ga sakon, uwargidan shugaban Najeriyar ta kuma wallafa wani sako na sauti mai tsawon minti 3:53, wanda a ciki ana iya jin wani mutumin da bai fadi sunansa ba yana sanar da wani mutumin da ya kira ‘Haji Abdurrahman’ labarin wani kamun da ‘yan sa-kai suka yi wa wasu barayin daji a yankin Tsafe da Mada na jihar Zamfara.

Karanta wannan  Ba Fashi: Duk Wanda Ya Zagi Allah ko Annabi SAW Hukuncin Kisa Ne Akansa Koda Ba Musulmi Ba Ne>>Sheikh Dr Sani Sharif Umar Bichi

A farkon sautin ana iya jin muryar wata mata da ke cewa, “Ga shi ku ji me yake fada…” Sai dai ba mu san ko muryar ta uwargidan shugaba Buhari ba ce.

Dan sauke manhajar hutudole a wayoyin ku. Sai a bi wannan link din na kasa:

Leave a Reply

Your email address will not be published.