fbpx
Tuesday, July 5
Shadow

Ajali! :Mota ta kutsa cikin gidan wata mata ta kasheta

Wata mata ta rasa ranta a wani hatsarin da ya afku a yankin Obada da ke Abeokuta, jihar Ogun.
Hadarin ya faru ne da misalin karfe 8:25 na safiyar ranar Litinin a kan babbar hanyar Legas zuwa Abeokuta.
An samu labarin cewa hatsarin ya rutsa da wata babbar motar Iveco, mai lambar rajista, KSF 209 XY.
Kakakin Rundunar Jami’an Kula da titi ta Jihar Ogun (TRACE), Babatunde Akinbiyi, ya ce manyan motoci biyu ne ke gasa, suna ta tukin ganganci kuma motar ta kubuci masu.
Daya daga cikin motocin, ana cikin haka sai ya kutsa kai cikin wani shago da gini, inda ya kashe matar.
Akinbiyi ya ce: “A cewar shaidun gani da ido, manyan motoci biyu suna tsere a kan layin, kamar a kan hanyar tsere lokacin da ba zato ba tsammani, a kokarin kauce wa wani abu, wanda ke kan layin ya bijire zuwa motar da ke ciki wanda kuma a kokarin gujewa na waje, ya kutsa kai cikin shago da gida a bakin hanya, inda ya kashe wata mata, wacce ta gama wanka, da kokarin shafa kayan kwalliya.
“Direban motar ya gudu don gujewa wasu mutane da ke neman kashe shi tare da cinnawa motar wuta, amma saboda gaggawar shiga tsakani na jami’an TRACE da ‘yan sanda daga Ofishin’ yan sanda na Obada-Oko, an tsaiwata fitinar.”

Dan sauke manhajar hutudole a wayoyin ku. Sai a bi wannan link din na kasa:

Karanta wannan  Nasan ku jajirtattu ne ku riga kora 'yan bindiga idan sun kawo maku farmaki, Gwamnan jihar Ondo ya fadaw 'yan jiharsa

Leave a Reply

Your email address will not be published.