(adsbygoogle = window.adsbygoogle || []).push({});
A baya ne hukumar kwallon kafa ta duniya, FIFA ta dakatar da Chelsea daga sayen ‘yan kwallo, bayan da aka sameta da laifin karya ka’idar sayen matasan ‘yan wasa.
An alakanta Chelsea da sayen ‘yan wasa da dama a watan Janairu ciki har da dan kwallon Paris St-Germain, Edinson Cavani da na Napoli, Dries Mertens.
Lampard ya fuskanci dalilin da ya sa suka kasa sayen ‘yan kwallo a Janairu da ya hada cewar kungiyoyi ne suka ki amincewa su sayar, ba laifin masu sayo ‘yan wasa a Chelsea ba ne.
Ziyech yana daga cikin wadan da suka ci wa Ajax kwallo a wasan da suka tashi da Chelsea 4-4 a Champions League a cikin watan Nuwamba.
(adsbygoogle = window.adsbygoogle || []).push({});
Ku biyomu a shafukanmu na sada zumunta dan samun labarai masu kayatarwa:
A shafin twitter zaku same mu a @hutudole
A shafin Facebook zaku samemu a @hutudolehausa
Danna nan dan sanin yanda zaku tallata hajarku a shafin hutudole