fbpx
Wednesday, August 10
Shadow

Akalla mutane 30 sun mutu yayin da 12 suka jigata sakamakon hadarin mota akan hanyar Kano zuwa Zaria

Akalla mutane 30 sun rasa rayukansu bayan da wani mummunan hadari ya faru akan hanyar Kano zuwa Zaria a kusa da Hawan Mai Mashi karamar hukumar Makarfi Kaduna.

Kuma mutane 12 sun jigata sosai yayin da su kuma aka garzaya dasu asibitin Shika dake karamar hukumar Zaria Kaduna.

Hukumar dake lura da ababen hawa akan titi ta FRSC tace hadarin ya faru ne sanadiyar gudu sosai da motocin keyi.

Kuma wannan mummunan hadarin ya faru ne a jiya ranar alhamis 21 ga watan Yuli.

Leave a Reply

Your email address will not be published.