Mahukunta a Saudi Arabia sun ce akalla mutum 1,301 ne suka rasu a yayin aikin Hajjin bana, kuma yawancinsu wadanda suka je ta barauniyar hanya ne da ke tafiyar kafa mai nisan gaske a cikin tsananin zafin da aka yi fama dashi a lokacin aikin Hajjin.
An gudanar da aikin Hajjin bana a cikin yanayi na tsananin zafi inda zafin a wasu lokuta kan zarta digiri 50 a ma’aunin selshiyos.
A cewar kamfanin dillancin labarai na SPA, fiye da rabin wadanda suka mutum ba su da cikakkun takardun da ke nuna cewa alhazai ne da suka je kasar ta Saudiyya don gudanar da aikin Hajjin bana.Kuma wahala da tsananin zafi ne ke sanya su galabaita saboda basu da wajen fakewa ma’ana inda ake tanadarwa alhazai.
Kamfanin dillancin labaran y ace yawancin wadanda suka mutun tsofaffi ne ko kuma masu fama da wat acuta mai tsanani.
Ministan lafiya na kasar, Fahd Al-Jalajel, ya ce tuni aka dauki dukkan matakan da suka dace don wayarwa da jama’a kai a kan illoli da ke tattare da tsananin zafi da kuma yadda alhazan za su kiyaye.
Ya ce, an yi wa kusan mahajjata dubu 500 magani, ciki har da mutum fiye da dubu 140 da suka shiga kasar ta barauniyar hanya inda kuma har yanzu akwai wadanda ke kwance a asibiti suna karbar magani.
Ana ta sukar Saudi Arabia a kan yin abin da ya dace don kula da alhazai, musamman wadanda basu da takardu kuma basu da yadda za sus amu na’urar sanyaya daki a inda suke da ma takaimemen wajen zama.
Cibiyar hasashen yanayi ta kasar a birnin Makka sai da yanayin zafin ya kai digiri 51.8 a ma’aunin Celsius.
Kasashe da dama sun bayar da cikakken bayanai a kan adadin mahajjatansu da suka rigamu gidan gaskiya, to amma duk da haka sai a ranar Lahadi Saudi Arabia ta fitar da cikakken bayani a hukumance a kan yawan alhazan da suka mutun.
Kamfanin dillancin labarai na AFP, ya rawaito jami’in diplomasiyya na cewa ‘yan kasar Masar 658 ne suka mutu.Sai Indonesia da ta ce ‘yan kasarta fiye da 200 ne suka mutu, yayin da India kuma ta ce adadin ‘yan kasarta da suka mutu a yayin aikin Hajjin bana saboda tsananin zafin sun kai 98.
Pakistan da Malaysia da Jordan da Iran da Senegal da Sudan da kuma Iraqi suma duk sun tabbatar da mutuwar alhazan nasu.
Ibadar Hajji ɗaya ce cikin rukunnan Musulunci biyar, kuma ana son duk wani Musulmi da ya samu dama ya je ɗakin Ka’aba mai tsarki don yin ta sau ɗaya a rayuwarsa.
Hukumomin ƙasar sun kiyasta cewa mutum miliyan 1.83 ne suka halarci aikin Hajjin Bana, inda miliyan 1.6 suka fito daga ƙasashen waje.
Firaiministan kasar Masar, Mostafa Madbouly, ya soke lasisin wasu kamfanonin jiragen sama da ke jigilar masu zuwa aiin Hajji ta barauniya 16.
Itama kasar Jordan ta kama aja-aja na kamfanonin shirya tafiye-tafiye da dama ta yi saboda jigilar alhazai ta barauniyar hanya.
Shi kuwa shugaban kasar Tunisiya, korar ministan harkokin addinai a kasar ya yi.