fbpx
Wednesday, August 10
Shadow

Akwai alama korona na shirin dawowa

Duk da cewa akwai manyan abubuwa da suka ɗauke hankalin duniya, kamar yaƙin da ake yi a Ukraine, amma da alama cutar korona na ƙoƙarin dawowa.

Alƙaluma na baya-bayan nan sun nuna cewa masu kamuwa da korona sun ruɓanya fiye da sau biyu a Birtaniya daga farkon watan Yuni.

Bayanai sun nuna cewa an samu kimanin mutum miliyan 2.3 waɗanda suka harbu da cutar.

Yanzu haka ana kuma fuskantar ƙalubalen sabbin nau‘ukan cutar, yayin da ake shakkun ko hukumomin lafiya za su iya cin galabarta.

Nau’ukan cutar da ke addabar mutane a yanzu su ne BA.4 da BA.5.

Nau’uka ne waɗanda suka rikida daga nau’in Omicron.

Omicron nau’in korona ne wanda yake da ƙarfin yaɗuwa a jikin ɗan’adam ya kuma raunana garkuwar da jiki ya samar na kare kai daga cutar.

To amma an gano cewa nau’in BA.4 da BA.5 sun fi shi haɗari.

Bayanai na nuna cewa yanzu haka Burtaniya na fuskantar ɓarkewa ta uku na cutar korona nau’in Omicron ke nan a cikin wannan shekarar.

Bincike ya nuna cewa sabbin nau’ukan korona na BA.4 da BA.5 suna iya bijire wa garkuwar da mutum ya samu bayan ya karɓi rigakafi ko kuma saboda ya yi fama da cutar a baya.

Dabarun da sabbin nau’ukan ke da su wajen harbar mutane da kuma raunin garkuwa daga cutar da ake samu a yanzu na nufin za a rinƙa samun ƙaruwar masu kamuwa da cutar.

Sai dai abin da masana ke cewa shi ne, kamewa daga cakuɗuwa da mutane ita ce babbar hanyar hana mutum kamuwa da mummunar rashin lafiya, ko kwanciya a asibiti, ko ma mutuwa a sanadiyyar korona.

Dan sauke manhajar hutudole a wayoyin ku. Sai a bi wannan link din na kasa:

Leave a Reply

Your email address will not be published.