fbpx
Monday, March 1
Shadow

Akwai Gurbacewar Tarbiyya a rayuwar ‘Yan Fim>>Farfesa Malumfashi

Masanin halayyar Dan’Adam din kuma malami a tsangayar halayyar daadam Farfesa Sani Lawan Malumfashi.

yace mutane su rika daukar dabiun masu kyau na cikin Fim ba halayyar su yan fim din ba.

 

Ya ce ana shirya Fim ne don Ilmantarwa da nishadantarwa da ya kamata jamaa su rika dauka tarbiyyar da za ta gyara su,ba wadda za ta lalata tarbiyya ba.

 

A wata hira da yayi da Freedom Kano Farfesa Malumfashi ya ce ina kira ga mutane wannan wannan sakon da yan fim suke turawa na kyaukwayon abinda ke faruwa a zahiri, shi ya kamata mutane su rika lura da shi, ba rayuwarsu ta kankansu ba (life styles) kenan, life styles din su dabiu ne da ya ke da illa ga mutane.

 

Ya kara da cewa ana kiran yan Fim da (Celebrity)shi kuma celebrity duk duniya suna da (lifestyles) dinsu wato tsarin rayuwarsu na daban da sauran mutane, wannan tsarin rayuwar shi ne matasanmu a yanzu suke maida hankalinsu akai ba sauraron sakon da suke isarwa ba.

 

Farfesa ya ce”idan ka kalli yadda tsarin ‘yan Fim suke gudanar da ruyuwarsu zaka samu matsalar gurbacewar rayuwa, amma kuma idan ka saurari sakon da suke nunawa al’umma to anan kuma zai amfani al’umma sosai wajen gyara rayuwarsu”

 

Ai kamar malam ne ance “ka saurari abinda Malam yake fada amma kada ka duba aikin malam”.

Dan sauke manhajar hutudole a wayoyin ku. Sai a bi wannan link din na kasa:


×
Kano

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *