Hukumar yaki da rashawa da cin hanci ta ICPC ta bayyana cewa, akwai kudaden da za’a gyara Najariya a cikin kasar amma wasu ne ke sacesu.
Tace ana tafka wannan sata ne a kullun wanda ke kawowa kasar cikas.
Shugaban hukumar, Professor Bolaji Owasanoye Ne ya bayyana haka a wajan wani taro.
Yace akwai hukumomi da yawa na yaki da rashawa sannan kuma akwai dokokin dake hana rashawa da cin hanci, saidai mutane ne basa yi musu biyayya.
Ya kara da cewa, rashawa da cin hanci na yiwa ci gaba karan tsaye sannan kuma yana taimakawa wajan kawo rashin dan haka dole a yakeshi.