Frank Lampard zai kara karawa da Jose Mourinho ranar lahadi yayin da Tottenham zata ziyarci Chelsea, kuma Chelsea tayi nasarar cin gabadaya wasannin data buga da Spurs tunda Lampard ya fara jagorancin kungiyar.
Lampard yaji dadin aiki a karkashin jagorncin Mourinho sosai a kungiyar Chelsea, yayin da suka yi nasarar lashe kofuna biyar a shekaru uku wanda suka hada da Premier league guda biyu da FA Cup da sauran su.
Lampard ya kawo karshen shekaru 13 daya yi yana wasa a Chelsea shekara 2014, bayan Mourinho ya kara dawowa kungiyar karo na biyu, kuma yanzu zasu kara hadu amma wannan karin fafatawa zasu yi a gasar Premier league.
Lampard ya bayyana akwai kyakkwar alaka tsakanin shi da Mourinhk amma aikin kocin daya ke yi da kuma takara a harkar wasan kwallon kafa ta fara kawo masu tangarda a cikin lamiran su, kuma duk da haka dai basu taba samun wata matsala ba.