fbpx
Saturday, September 23
Shadow

Akwai Na kusa da shugaba Buhari da basa son ayi zabe, so suke su masa sagegeduwa a kafa gwamnatin rikon kwarya>>Gwamna El-Rufai ya tona Asiri

Gwamna Nasiru Ahmad El-Rufai na jihar Kaduna ya bayyana cewa, akwai na kusa da shugaba Buhari dake son kawowa Dimokuradiyyar Najariya tangarda.

 

Ya bayyana hakane a hirar da aka yi dashi a gidan jaridar Premium times inda yace basa son a yi zabe, so suke a kafa gwamnatin rikon kwarya.

 

Gwamna El-Rufai yace, ‘yan takara biyu ne suka so su ci zabe amma basu samu ba, watau Lawal Ahmad ko kuma gwamnan bankin Najariya, watau Godwin Emefiele.

 

Gwamnan ya kara da cewa, baya tsoron kowa kuma irin wadannan mutane a bayan shugaba Buhari ne kawai zasu iya lafewa su samu abinda suke so dan kuwa basu iya siyasa ba kuma ba zasu iya cin zabe ba.

 

Saidai be bayyana sunayen wadannan mutanen ba.

Dan sauke manhajar hutudole a wayoyin ku. Sai a bi wannan link din na kasa:

Talla: Danna nan dan samun gagarumar kyauta

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *