Wednesday, June 3
Shadow

Akwai tsarin bude Makarantu Kwanannan>>Gwamnatin Tarayya

Gwamnatin tarayya ta bayyana cewa tabbas akwai shirin bude makarantu kwanannan amma ba nan da sati 2 ba kamar yanda wasu ke yadawa.

 

Karamin ministan Ilimi, Chukwuemeka Nwajiuba ne ya bayyana haka ga manema labarai a yayin da kwamitin yaki da cutar Coronavirus/COVID-19 ke bayani a jiya,Juma’a.

Yace suma suna so ace an koma makaranta amma ba zasi so saka rayuwar yara cikin jadari ba.

 

Yace akwai tsarin dawowa da makarantu kwanannan amma ba nan da sati 2 ba kamara yanda maganar ke yawo ba, yace sai sun hana da masana sun basu tabbacin cewa yaran zasu iya komawa makaranta ba tare da barazanar cutar Coronavirus/COVID-19 ba tukuna.

Dan sauke manhajar hutudole a wayoyin ku. Sai a bi wannan link din na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=hdlabarai.aplibwxLeave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *