Sunday, March 29
Shadow

Akwai yiyuwar fadawa matsalar karancin man fetur saboda fara zaman gida da kungiyar dillalan man zata yi

Kungiyar dillan mai ta NUPENG ta bayyana cewa idan ba’a dauki matakin baiwa membobinta kariya ta musamman daga cutar corona/covid19 ba to zata dauki matakin baiwa membobin nata umarnin zama a gida.

 

Hakan ya fito ne daga bakin shugaban kungiyar,Willimas Eniredonana Akporeha da sakataren kungiyar,Afolabi Olawale a sanarwar da suka fitar ga manem labarai Ranar Talata.

 

Kungiyar tace membobinta na aiki na musamman wajan bautawa Al’umma amma kuma dilene ta dauki matakin karesu.

 

Kungiyar tace nan da ranar juma’a ne zata baiwa membobinta umarnin zama a gida saboda kare kansu daga cutar ta Coronavirus/COVID-19

Dan sauke manhajar hutudole a wayoyin ku. Sai a bi wannan link din na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=hdlabarai.aplibwx

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *