fbpx
Thursday, August 18
Shadow

Akwai yiyuwar Gwamnati ta fara Amfani da Otal da Makarantu a matsayin guraren killace masu Coronavirus/COVID-19

Gwamnatin tarayya ta bayhana cewa akawai yiyuwar ta fara amfani da Makarantu da Otal wajan killace masu cutar Coronavirus/COVID-19.

 

Ministan lafiya, Osagie Ehanire ne ya bayyana haka ga manema labarai a ganawar da yayi dasu a lokacin da kwamitin gwamnatin tarayya dake yaki da cutar ke bayyana halin da ake ciki.

Yace duk da ba’a kai wannan matsayi ba amma makarantu da Otal su shirya dan za’a iya amfani dasu a matsayin wajan killace masu Coronavirus/COVID-19 idan cutar ta yi kamari ta yanda hakan zai gagari guraren killacewar da gwamnati ta tanada.

Karanta wannan  Shugaba Buhari ya nada Aliko Dangote a matsayin shugaban sabuwar kungiyar da zata kawo karshen cutar Malaria a Najeriya

 

Ministan na maganane musamman akan jihar Legas da aka samu mutane sama da Dubu 4 masu dauke da cutar.

Dan sauke manhajar hutudole a wayoyin ku. Sai a bi wannan link din na kasa:

Leave a Reply

Your email address will not be published.