Wata majiya ta bayyana cewa, Kakakin Majalisar Dattijai, Sanata Ahmad Lawal ka iya shiga jerin masu neman takarar shugaban masa a 2023.
Wani na kusa da Sanata Ahmad Lawal ne ya bayyanawa majiyar tamu wannan labari.
Yace dalili haka shine, ba lallai sanata Lawal ya sake samun damar zama shugaban majalisa ba bayan shekarar 2023.
Shiyasa zai yi amfani da wannan damar musamman idan jam’iyyar APC ta bar tikitin neman shugaban kasa kowa ya nema ba tare da cewa ‘yan kudu ne kawai zasu nema ba.
Saidai kawunan ‘yan jam’iyyar ya rabu inda wasu ke ganin kamata yayi a bar tikitin kowa ya nema, irin masu wannan ra’ayi, akwai gwamnan jihar Kogi, Yahya Bello.