Tsohon ministan kudi na lokacin mulkin soji a zamanin Ibrahim Babangida, Olu Falae yace dakyar ‘yan bindiga da Boko Haram su bari a ayi zaben shekarar 2023.
Ya bayyana hakan ne yayin dayake ganawa da manema labarai inda yace masu harin da ‘yan ta’addan ke kaiwa yayi kamari sosai a fadin Najeriya.
Domin sun babbaka ofisoshin hukumar zabe ta INEC kuma sun kaiwa babban gidan kurkukun Najeriya hari na Kuje ind suka saki mutane da dama dake ciki.
A karshe dai yace koda ace angudanar da wannan zaben a shekarar 2023 to sakamakon ba zai taba yiwa ‘yan kasa dadi ba.