fbpx
Wednesday, August 10
Shadow

Akwai yiyuwar zaku fada cikin bakin talauci saboda tsadar kayan abinci>>Gwamnatin tarayya ta gargadi ‘yan Najeriya

Gwamnatin tarayya ta yi gargadin cewa idan ba’a dauki matakin da ya dace ba, da yawan ‘yan Najeriya zasu fada cikin matsalar talauci saboda tsadar kayan abinci.

 

Ministan Noma, Dr. Mohammad Abubakar ne ya bayyana haka a babban birnin tarayya, Abuja a wajan wani taro da aka yi.

 

Saidai yacs tsadar abincin ba Najeriya kadai ta shafaba, ta shafi sauran kasashen Duniya, kuma matsalar canjin yanayi ne ya kawo ta.

 

Ya bayyana cewa, matsalar canjin yanayin zata shafi harkar noma da kuma samar da abinci dan kuwa akwai alamar fari da sauran matsaloli.

Leave a Reply

Your email address will not be published.