fbpx
Tuesday, May 24
Shadow

Al-ummomin garuruwan Medu, Danmadai da Kanyu sun sauke Al-qur’ani Mai girma domin Allah ya kwato masu hakkinsu akan gwamnatin jihar Jigawa

A yau Asabar 22 ga watan Ramadan wanda yayi daidai da 23 ga watan Afrilu 2022, al-ummomin garuruwan Medu, Danmadai, Kore balatu,Kore babba, gayawar malam, kagadama, Garin chiroma, da fulaninsu sun gabatar da Sallah nafila da saukar Al-qur’ani Mai tsarki domin Allah ya kwato masu hakkinsu akan gonakinsu da gwamnatin jihar Jigawa ta karbe masu.

Idan ba ku manta ba a ranar 3 ga watan Afrilu mun kawo maku labarin mutanen wadannan yankin da suka gabatar da Al-qunut kan gonakinsu da suke zargin gwamnatin jihar Jigawa ta hada baki da wani mutumin kasar china Mai suna Mista Lee mai kamfanin GNA (Great Northern Agribusiness Company), wanda shi ne suke zargin ana sayarwa da gonakinsu da aka karbe masu.

Al-ummomin sunce ana karbe masu gonaki a basu kudaden da ba su taka kara ba, a zantawa da wani dattijo da ya nemi a sakaya sunansa, yace duk shekta (Hecta) guda suna sayar da ita akan N95,000 amma ita Gwamnatin Jihar Jigawa bai fi ta baiwa mutum N30,000 akan shekta guda ba.

A bisa haka suka yanke shawarar yin sallolin nafilfili, Al-qunut da karatun Al-qur’ani Mai gida domin Allah ya kawo masu dauki.

Dan sauke manhajar hutudole a wayoyin ku. Sai a bi wannan link din na kasa:

Leave a Reply

Your email address will not be published.