fbpx
Monday, March 1
Shadow

Ala’adar yin Lefe ne ke kawo mutuwar aure a Arewa>>Sheikh Bin Uthman

Fitaccen Malamin addinin musuluncin nan sheikh muhd bin Usman da ke Kano, ya ce yawaitar mutuwar aure da ake samu a arewa ya samo asali ne daga tsawwalawa da ake yi na kayan lefe ga samari, inda ya ce musulunci bai shardanta yin kayan lefe ba.

 

A wata hira da ya yi da Freedom FM a yau ya ce mafi yawan lefen da ake kawowa yana zama riya ne, ga kuma rikici da ya ke haddasawa kuma daga nan ya ke bude kofar fitina.

 

Bin Usman ya kara da cewalefe wata alada ce da ya kamata a soke kwata-kwata, sannan ya bada misalin wani da ya kashe miliyan 1.5 akan lefe aka tatike gaba daya, da ya tsahi kama haya ya kama na dubu 200 mahifiyar yarinyar ta ce baa isa ba ‘yarta ta fi karfin wannan gidan.

 

“Namiji zai iya sayen kayan sawa ya ajiye a gidansa idan ta zo sai ya bata amma kawowa gidansu yarinya fitina” a cewar bin Usman.

 

Amma ya ce idan namiji shi da kansa ya ga yana da hali da zai iya yi ba matsala, amma kar iyaye su ce dole sai anyi su barshi a matsayin zabi, dama abinda ake so shi ne a kore takurawa da matsawa.

Dan sauke manhajar hutudole a wayoyin ku. Sai a bi wannan link din na kasa:


×
Kano

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *