Wannan hoton wutar da kuke gani wani dutse ne da yake ta faman ci da wuta har tsawon shekaru 65.
Shidai wannan dutsen sunansa Yanar Dagh dake kasar Azarbaijan.
Shidai wannan dutse mai abun mamaki, wata gobara ce ta iskar gas take ci gaba da ci a jikinsa tsawon shekaru 65 ba lafawa.
Dutsen yana wani tsauni da ke gabar tekun Absheron da kuma Tekun Caspian dake kusa da Baku, babban birnin kasar ta Azarbaijan.
Harshen wutar dake ci a cikin dutsen yana tashi sama a cikin iska kusan nisan mita uku.
Duk mai son kallon bidiyon wannan Dutsen kai tsaye ya shiga wannan link din.
👇👇
https://bit.ly/3wq1p8c
Daga Mukhtar Lawan Liver Gwarzo