AL’AJABI: Ko Kun San Garin Da Mata Ne Kawai Suke Sarauta A Arewacin Nijeriya?
Shin kun taɓa sanin cewa, akwai wata masarauta da mata zalla ke mulki a arewacin Nijeriya?
Masarautar Dingep da ke Ƙaramar Hukumar Ganye a jihar Adamawa a arewa maso gabashin ƙasar ta shafe sama da ƙarni Bakwai ƙarƙashin jagorancin mata, wani abu da ya sha bambam da sauran masarautu da ke arewacin ƙasar.
Garin ya na da yawan jama’a sama da mutum Ɗari Biyar, kuma sarauniya ce ke gudanar da dukkan aikace-aikace da sarakunan gargajiya maza ke yi a wasu masarautun.
Har kawo wannan ƙarni na Ashirin da Ɗaya (21st century) da ake ganin duniya ta ci gaba da wayewa ta fuskoki da daman gaske, ake kuma ganin akwai sabon salo na rayuwa, kama daga harkar ta fi da mulki zuwa sauran sha’anin rayuwa, a ɓangaren masarautun gargajiya ba a rasa masarautun da suke ƙarƙashin kulawa da ikon mata ba har yanzu.
Tarihi
Ɗaya daga cikin irin waɗannan masarautu dai itace masarautar Arnado Debbo da ke ƙarƙashin masarautar Ganye a jihar Adamawa, in da a tarihin kafuwa da ci gaba da wanzuwar masarautar; Mata ne ke shugabancin masarautar a kuma zauna lafiya.
Kamar yadda masana tarihin masarautar suka bayyana, ba a taɓa samun namiji da ya shugabanci masarautar kuma ya yi tsawon rai ba.
Ma’anar kalmar “Arnado Debbo” da Fulatanci shi ne (Jagorancin Mace) wadda kuma ita ce kalmar da garin ya samo sunansa, a don haka a tarihin tsawon kafuwar garin ya ci gaba da amsa wannan suna sakamakon sarautar da mata ke yi.
Masarautar Arnado Debbo dai, daɗaɗɗiyar masarauta ce mai cike da tarihin gaske, don kuwa ita ce sila da salsalar kafuwar masarautar Ganwari Ganye har ma da samuwar garin Ganye baki ɗaya, kana ta ƙunshi wasu gundumomi da suke ƙarƙashinta da suka haɗa da Dimaeb, Dapellum, Sayikmi, Dauera, Naburapeu, Dimkolum, da Samjerum.
Wani abin mamaki shi ne, kusan kashi 70 bisa 100 na jama’ar masarautar Musulmi ne, wadda ba kasafai ake samun mace ta yi shugabanci a cikinsu ba musamman ma kan sha’anin sarauta.
Daga Taskar Nasaba