Monday, October 14
Shadow

Alamomin ciwon zuciya

Ciwon zuciya ya danganta da irin zuciyar, akwaishi kala-kala.

Dan haka bari mu bayyana alamomin ciwon zuciya daban-daban.

Akwai wanda ake kira da Coronary artery disease: Wannan kalar ciwon zuciya ne dake taba hanyoyin dake baiwa zuciyar jini.

Wannan kalar ciwon zuciya shine wanda yafi kama mutane kuma yakan kai ga Bugawar Zuciya da ke iya kaiwa ga mutuwa, Yakan kuma kai ga ciwon kirji, ko shanyewar rabin jiki.

Alamomin wannan ciwon zuciya ya banbanta a tsakanin mata da maza, misali, idan ya kama maza, zasu iya fuskantar ciwon kirji, yayin da idan ya kama mata, zasu iya fuskar Ciwon kirjin da karin wasu matsaloli da suka hada da numfashi sama-sama, da yawan zazzabi da safe da kuma matsananciyar kasala.

Karanta Wannan  Kalli Bidiyo yanda wata Zundumemiyar Budurwa ta ruga da gudu zata rungume gwamnan Kano, Abba Gida-Gida

Ga dai alamomin ciwon zuciya na Coronary artery disease dake damun maza da mata jimulla:

Ciwon kirji, ko matsewar kirji, kwata-kwata za’a ji kirjin babu dadi.

Yin numfashi sama-sama.

Ciwon wuya, muka-muki, makogoro, ciwon saman ciki da ciwon baya.

Ciwon jiki, Jin wani bangaren na jikinka kamar ba a jikinka yake ba, zaka ji kafarka ta yi sanyi, zaka iya jin kafadunka ma sun yi sanyi.

Akwai kuma ciwon zuciya saboda rashin bugawar zuciyar yanda ya kamata, zata iya bugawa da sauri, ko a hankali ko kuma ta rika yin aiki ba yanda ya kamata ba:

Ciwon kirji ko rashin jin dadi.

Juri.

Suma.

Jin rugugi a kirji.

Jin kanka ba nauyi.

Karanta Wannan  Ji Farashin da Dangote zai sayar da man fetur dinsa

Bugawar zuciya da sauri sosai.

Numfashi sama-sama.

Bugawar zuciya a hankali.

Akwai kuma ciwon zuciya da ake cewa, congenital heart defects. Shi wannan kalar ciwon zuciya yawanci ana haihuwar mutum dashi ne.

Alamomin wannan ciwon zuciya me suna congenital heart defects a jikin yara ya hada da:

Fatar yaro ko lebensa zai canja kala.

Kafafuwansa zasu iya kumbura.

Cikin yaro zai iya kumbura.

Gefen idanunsa zai iya kumbura.

Yaro zai iya yin fama da numfashi sama-sama yayin da ake bashi abinci.

Yaro zai iya zama shagwal ba nauyi.

Idan kalar wannan ciwon zuciya bai yi tsanani ba, ba lallai a ganeshi da wuri ba har sai yaro ya girma ko kuma ya zama babban mutum:

Alamomin wannan ciwon zuciya da bai da illa sosai sun hada da.

Karanta Wannan  BABU INDA DANGIN MIJI SUKA TAƁA SAKIN MATA DAN HAKA AMINU ADO YA DAWO KUJERARSA, CEWAR RASHEEDA MAISA’A

Saurin daukewar numfashi yayin da ake motsa jiki.

Saurin gajiya yayin motsa jiki.

Kumburar hannu, gwiwa, idon sawu da tafin kafa.

Akwai kuma kalar ciwon zuciya da ake cewa, cardiomyopathy wanda bai cika nuna wata illa sosai ba sai idan yayi tsanani.

Idan wannan kalar ciwon zuciya me suna cardiomyopathy yayi tsanani za’a iya ganin matsaloli kamar haka:

Juwa, rashin jin nauyin kai, da suma.

Kasala.

Daukewar Numfashi yayin da ake motsa jiki da yayin da ake zaune.

Daukewar numfashi yayin da ake shirin yin bacci da yayin da aka tashi daga bacci.

Jin bugun zuciya da sauri sosai.

Kumburar kafa, Idon sawu, da tafin kafa.

2 Comments

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *