Tuesday, June 18
Shadow

Alamomin shigar ciki a satin farko

Wadannan bayanai na kasa sune alamomin dake nuna cewa kin dauki ciki a satin Farko.

Saidai ki sani mafi yawan mata basa ganin ko wace irin alama a satin farko bayan sun dauki ciki.

Saidai wasu matan kuma suna ganin alamomin daukar ciki a satin farko kamar su kasala, ciwon nono, da ciwon gabobi a kwanki 5 zuwa 6 bayan an yi jima’i.

Yawanci likitoci suna yin gwajin ciki ne sati daya bayan daukewar jinin al’ada.

Maganar gaskiya shine ganin alamun shigar ciki a satin farko bai cika faruwa ba ga mafi yawan mata amma kowace mace da irin jikinta.

Ga dai alamun da mace zata iya gani a satin farko wanda ke nuna alamar ta dauki ciki:

Karanta Wannan  'Tattalin arziƙin Najeriya na bunƙasa'

Rashin Ganin jinin Al’ada.

Zubar da jini, ba irin na al’ada ba, zai iya zuwa kadan kuma zai iya daukar kwanaki.

Za’a iya jin ciwon ciki, ciwon baya da sauransu.

Kasala.

Yawan fitsari.

Ciwon kai.

Shiga damuwa.

Rashin son cin abinci.

Mata da yawa zasu iya daukar ciki ba tare da ganin wadannan alamomi ba. Babbar hanyar tabbatar da an dauki ciki shine a yi gwaji.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *