fbpx
Saturday, September 23
Shadow

Alamomin so na gaskiya

Alamomin so na gaskiya suna da yawa, amma ga muhimmai a cikinsu kamar haka:

  • Kyauta
  • Yabo
  • Son kasancewa tare
  • Tunawa da wanda ake so yayin da ake nesa da juna
  • Girmamawa
  • Kishi
  • Farin ciki da nasarar wanda ake so
  • Bakin ciki yayin wata matsala ta samu wanda ake so.
  • Son ganin ci gaban wanda ake so

Bari mu fara bayani akansu kamar haka:

Kyauta

Kyauta na da matukar muhimmanci a soyayya, bawai sai kudi me yawa ba, ko kuma abu me girma ba, duk wanda yake son wani so na gaskiya, zai ji yana son yi masa kyauta dan birgeshi.

Yabo

A yayin da so ya kai so, to zaka ga ana yawan yabon wanda ake so a gabanshi ko a bayan idonshi, ba za’a so wani ya aibatashi ba.

Son Kasancewa tare

Wanda ke maka soyayyar gaskiya, a ko da gaushe zai so kasancewa tare da kai, ba zai kosa da kai ba.

Tunawa da wanda ake so yayin da ake nesa da juna

Duk wanda ke sonka da gaskiya, ko da yayi nesa da kai, zai rika bege da tunaninka da kuma yawan nemanka a waya kuna gaisawa.

Girmamawa

Wanda ke maka so na gaskiya ba zai tozarta ka ba, zai rika girmamaka yana ganin ka a matsayin mutum me mutunci. Zai rika gaskata maganarka, ko da kuwa sauran mutane suna karyata ka.

Kishi

Duk me sonka da gaskiya, zai yi kishinka, ba zai so ya ganka kana tarayya da wani wanda zai raba ku ba, ko kuma kana tarayya da wani wanda baku dace da juna ba.

Farin ciki da nasarar wanda ake so

Duk me sonka da gaskiya, zai yi matukar farin ciki da duk wata nasara da ka samu a rayuwa, zai zama gaba-gaba wajan nuna jin dadinsa.

Bakin ciki yayin wata matsala ta samu wanda ake so.

Idan ka shiga matsala, ko da kowa ya gujeka, masoyinka na asali zai kasance tare da kai ya tayaka bakin ciki, kuma ya debe maka kewa.

Son ganin ci gaban wanda ake so

Duk me sonka da gaskiya zai so ganin ka ci gaba a rayuwar Duniya da lahira, zai rika baka shawarwari na gari.

Dan sauke manhajar hutudole a wayoyin ku. Sai a bi wannan link din na kasa:

Talla: Danna nan dan samun gagarumar kyauta

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *