Watakila kinga canji a jikinki kin fara tambayar me ya faru? Ko kuma watakila batan wata ko daukewar jinin al’adane kadai kika fuskanta.
Wasu matan na ganin alamun shigar ciki a watan Farko yayin da wasu basa gani.
Ga alamun da ake gani na shigar ciki a watan Farko:
Rashin zuwa jinin Al’ada ko batan wata: Musamman idan kina ganin jinin al’adarki akai-akai amma baki ganshi ba wannan karin, zai iya zama kina da ciki.
Canjawar Dabi’a: Zai zamana kina saurin fushi ko kuma haka kawai ki rika jin bacin rai, hakanan zai iya zama kina dariya akan abinda bai kai ayi dariya akansa ba.
Cikinki zai rika kuka ko kuma kiji kamar kinci abinci: Cin abinci irin su Aya, Tuwon masara, dawa, ko gero wanda ba’a barza ba, Kwakwa, wake zasu taimaka miki magance wannan matsalar.
Zaki ji gabobinki na daddaurewa suna miki ciwo wani lokacin, idan hakan na faruwa dake kuma yana damunko, ki gaggauta gayawa likitanki.
Jini zai iya diga kadan wanda kan iya bata miki wando, idan an ga hakan, zaki iya saka audiga ko Liner dan kada ya rika bataki, ba jinin al’ada bane.
Yawan fitsari: Idan kika samu ciki, yawan jinin jikinki na karuwa kuma hakan na samar da fitsari akai-akai. Wannan matsala ta kan dade bata gushe ba.
Nononki zai rika zafi, hakan na faruwa ne saboda canje-canje dake faruwa a jikinki. Saidai ana tafiya hakan na raguwa.
Zaki rika jin gajiya ko kasala.
Jin alamun rashin lafiya, musamman da safe, saidai wasu basa fuskantar wannan matsala. Abubuwan dake taimakawa magance wannan matsala sun hada da shan ruwa ko shayin citta, Shan multivitamins da kuma shan ruwa.
Zaki iya fuskantar wahala wajan yin bayan gida ko kashi, idan kinji hakan, ki tuntubi Likita.
Rashin son cin Abinci: Zaki ji baki son warin wasu daga cikin abinci dan haka zaki iya rage cin abinci, ana iya magance matsalarnan wajan amfani da fanka a dakin dafa abinci, da kawar da abincin da baki son kanshinshi daga kusa dake da sauransu.
[…] yawa daga cikin Alamomin farko da kika fara ji na daukar ciki zasu daina damunki bayan da cikinki ya kai watanni […]