fbpx
Monday, August 15
Shadow

Alfarma watan Ramadan ne yasa muka sako manajan-darakta na bankin manoma – Yan bindiga

‘Yan ta’addan da suka kai hari kan jirgin Abuja zuwa Kaduna a ranar 28 ga Maris, 2022, sun ce an sako Manajan Daraktan Bankin Noma (BoA) Alwan Ali-Hassan bisa nuna tausayi.

A wani faifan bidiyo dake yawo a shafukan sada zumunta, daya daga cikin ‘yan ta’addan da ya yi magana da harshen Hausa, ya ce sun yanke shawarar yi wa BOA MD rahama ne bisa la’akari da lokacin watan Ramadan da shekarunsa.

Hassan, wanda ‘yan ta’addar dauke da muggan makamai suka yi masa baya kafin a sake shi, ya kuma tabbatar da cewa sun sake shi ne bisa dalilai na tausayi.

BoA MD, wanda aka umurce shi da ya yi magana a cikin faifan bidiyon kafin a sake shi, ya roki gwamnati da ta saurari ‘yan ta’addan domin a sako sauran wadanda aka kama.

Dan sauke manhajar hutudole a wayoyin ku. Sai a bi wannan link din na kasa:

Leave a Reply

Your email address will not be published.