fbpx
Thursday, July 7
Shadow

Ali Nuhu da Adam A. Zango sun aikewa da General BMB kudi bayan gini ya fada masa a kafa

A baya ne muka ji yanda gini ya fadawa tauraron fina-finan Hausa,  Bello Muhammad Bello a kafa inda har aka masa gyara.

 

Bellon ya godewa duka wanda suka tayashi jaje na ‘yan uwa da abokan arziki. Daga cikin wanda yawa Godiya akwai Sani Musa Danja, Ado Gwanja, Afakallahu da Sauransu.

 

Bello ya kuma godewa Ali Nuhu inda yace yana godiya bisa kiransa da yayi da kuma kudin da ya aika masa.

 

Hakanan Bello Ya kuma godewa Adam A. Zango inda shima yace yana godiya da nuna damuwa da halin da ya shiga sannan kuma da kudin da ya aika masa.

 

Ya bayyana cewa shi dan APC ne, Adam A. Zango kuma dan PDP amma hakan bai hanasu zumunci ba.

 

Dan sauke manhajar hutudole a wayoyin ku. Sai a bi wannan link din na kasa:

Leave a Reply

Your email address will not be published.