fbpx
Thursday, July 7
Shadow

Ali Nuhu da Adam A. Zango sun yabi juna

Taurarin fina-finan Hausa,  Ali Nuhu, Sarki da Adam A. Zango, sun yabi juna a shafukansu na sada zumunta.

 

A baya dai an samu rashin jituwa tsakanin jaruman biyu, inda mabiyansu suka rika jifar juna da maganganu,  amma ga dukkan alamu a yanzu lamarin ya wuce.

 

Ali Nuhu ne ya rubuta yabon Adam a Zango  ta shafinsa na Instagram  inda ya bayyanashi da cewa Yarimana. Haduwar Aboki da kuma dan uwa abu ne na musamman. Daya muke kuma babu bukatar bayani akan hakan. Ina matukar girmamaka bisa irin yanda muka kasance da kuma zamu ci gaba da kasancewa tare yarimana.

 

https://www.instagram.com/p/CH2wcYBhESH/?igshid=rd36ynmrw6g0

 

A nasa bangaren, Adam A. Zango shima yayi Nashi rubutun inda yace abubuwa da yawa sun faru tsakanin ‘yan uwan juna da suka dade tare. Kuma dolene a samu tangarda amma zai wuce kuma su ci gaba da kasancewa ‘yan uwan juna. Haka yake tsakanina da kai(Ali Nuhu), ina godiya bisa kasancewa dan uwana kuma shugabana.

 

https://www.instagram.com/p/CH2srebnlDS/?igshid=1pp4wgrz0epft

Dan sauke manhajar hutudole a wayoyin ku. Sai a bi wannan link din na kasa:

Leave a Reply

Your email address will not be published.