fbpx
Saturday, August 8
Shadow

Alkalin Alkalai ya bada umarnin rufe kotuna

Alkalin Alkalai na Najeriya,Muhammad Tanko ya baiwa kotunan dake kasarnan umurnin dasu kulle daga ranar Talata, 24 ga watan Maris saboda dakile yaduwar cutar Coronavirus/COVID-19.

 

A wata sanarwa daya fitar, Muhammad Tanko ya bayyana cewa cutar ta Coronavirus/COVID-19 da bata da magani a halin yanzu zata zamarwa kotunan kasarnan Barazana lura da cewa ana gudanar da zaman shari’a ne da mutane da yawa.

 

 

Yace dan haka za’a ci gaba da zaman kotu amma a bi shawarar hukumar kula da cututtuka ta Najeriya, NCDC na cewa kads mutane sama da 50 su taru a waje 1.

 

Yace a jihohin da aka saka wata doka ta daban ba wannan ba to kotunan su bi dokokin jihohin da suke.

Dan sauke manhajar hutudole a wayoyin ku. Sai a bi wannan link din na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=hdlabarai.aplibwxLeave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *