Alkalin alkalai na kasa Ariwoola zai riga daukar albashin naira miliyan goma a kowan wata bayan kotun babban birnin Abuja ta bukaci a karawa akalai albashi.
Mai shari’a Obaseki ne ya bayyana hakan ranar juma a babbar tarayyar inda yace su kuma sauran manyan alkalan kotun koli sai a riga biyan su naira miliyan tara.
A kwanakin baya ne shugaban kasa Muhammadu Buhari ya rantsar da Ariwoola a matsayin alkalin alkalai na wucin gadi, bayan Muhanmad Tanko yayi murabus.