Tsohon gwamnan Legas kuma Jigo a jam’iyyar APC, Bola Ahmad Tinubu ya bayyana cewa, alkawuran da tsaffin Shuwagabannin Najeriya suka yi ba’a cika su ba.
Ya bayyana hakane a wajan taron da matasa suka yi dan nuna mai goyon baya a jihar Legas.
Tinubu yace babu ta yanda za’a kira matasan Najeriya da ragwaye bayan ba’a basu abinda zasu dogara da kansu ba ko kuma ba’a samar musu yanayi me kyau na kafuwa ba.
Yayi alkawarin samar da wutar Lantarki da kuma samar da Ilimi kyauta idan aka zabeshi a matsayin shugaban kasa.