Tauraron fina-finan Hausa kuma mawaki, Adam A. Zango har yanzu yana kara nuna jin dadi, godiya da mamakin irin yawan masoyanshi daya gani a kasar Kamaru, ya bayyana cewa shi “wallahi be san ya kai hakaba”, a cikin satin daya gabatane Adamun yaje yin wasa a kasar kuma mutane kimanin dubu goma suka cika gidan wasan da aka gayyaci Adamun, hakan yasashi farin ciki sosai.
A wani sako daya fitar ta dan dalinshi na sada zumunta da Muhawara, Adam yayi fatan cewa Allah yasa ya samu irin wannan jama’ar ranar da za’awa gawarshi sallah.
Ga abinda ya rubuta kamar haka.
“Gani ya kori ji, ….wallahi bansan na kai haka ba… Allah ka karawa Annabi daraja!!Allah ka barni da masoyana…Allah kasa in samu jama’a haka a ranar sallar gawata”.
Amin Adamu.
Haka kuma Adamun ya hadu da manyan mutane a zuwan nashi kasar ta Kamaru, anan shine tare da shugaban ‘yan sanda na filin jirgin saman kasar.