fbpx
Saturday, August 20
Shadow

Allah Sarki: Iyalan Wani bawan Allah da ya rasu sun mayarwa da Gwamnati Albashin da ya ci ba bisa ka’ida ba

Iyalan wani bawan Allah da ya rasu me suna Baba Aji Mamman a jihar Yobe sun mayarwa da Gwamnatin jihar Miliyan 11 na Albashin da ya ci ba bisa ka’ida ba.

 

Mamacin kamin ya rasu yayi fama da jinya inda dalilin haka da kuma tsufa yasa yake zuwa aiki sau 2 ko 3 kacal a mako maimakon sau 5.

 

Saidai kamin ya rasu, ya barwa ‘ya’yansa wasiyyar cewa, su lissafa kudin Albashin da ya ci na rane kun da bai je aiki ba su mayarwa da gwamnati.

Karanta wannan  Labari me dadi: An kwato buhunan takin zamani da 'yan ta'adda suka siya dan hada bamabamai

 

Kuma cikin ikon Allah sun samu kudin da suka kai Miliyan 11 suka kuma mayarwa da gwamnati.

 

Yayi aiki ne da hukumar sanya wutar lantarki a kauyukan jihar Yobe, ‘ya’yan nasa sun mayar da kudin sannan suka kuma baiwa gwamnatin hakuri kan abinda mahaifin nasu ya aikata.

Dan sauke manhajar hutudole a wayoyin ku. Sai a bi wannan link din na kasa:

Leave a Reply

Your email address will not be published.